Hukumar kiwon lafiya matakin farko ta jihar Jigawa ta kulla yarjejeniya da masu motoci sama da 600 don jigilar mata masu juna biyu zuwa duk wani asibiti da ke kusa.

Daraktan hukumar, Dr Abdulqadir Yakubu shine ya bayyana hakan yayin wani taro a karamar hukumar Kiyawa da kungiyar Save the Children International ta shirya a Kwalejin Gwamnatin Tarayya dake Kiyawa.

Dr Yakubu ya ce kungiyar Save the Children International karkashin shirin INSPIRING za ta tallafa wa shirin kuma an shigar da yara ‘yan kasa da shekaru biyar wanda ke bukatar duk wani daukin gaggawa.

A cewarsa, a karkashin shirin, mazauna al’umomi ne suka zabo masu motocin kuma gwamnati ta tantance su.

Ya ce gwamnatin jihar tana da kudade na musamman a Asusun hukumar don wannan aikin, kuma za a rika biyan masu motocin kowane wata gwargwadon yawan jigilar da suka yi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: