Gwamnatin Jihar Jigawa ta nanata kudurinta na kawo karshen ciwon dabbobi

0 78

Gwamnatin Jihar Jigawa ta nanata kudurinta na yin hadin gwiwa da Kungiyar Kwararrun Likitocin Dabbobi ta Kasa reshen Jihar nan.

Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jiha Alhaji Hussaini Ali Kila, shine ya bayyana hakan a lokacin da jagorocin Kungiyar suka kai masa ziyara girmamawa a Ofishinsa.

Tun farko a Jawabin sa, shugaban kungiyar, Dokta Ya’u Muhammad ya ce sun kai ziyarar ne a wani bangare na ganawa da masu ruwa da tsaki da sauran hukumomi masu alaka da kungiyar.

Shugaban kungiyar ya bayyana gamsuwa bisa goyon baya da ofishin shugaban ma’aikatan ke baiwa kungiyoyin kwararru, inda yayi fatan hakan zai dore.

Alhaji Hussaini Ali Kila ya bayyana farin ciki bisa wannan ziyara, tare da baiwa kungiyar tabbacin samun hadin kai da goyon bayan ofishin sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: