Gwamnatin jihar Jigawa ta raba babura 27 ga shugabannin kungiyar mahauta na kananan hukumomin jihar 27

0 73

Gwamnatin jihar Jigawa, ta raba babura 27 ga shugabannin kungiyar mahauta na kananan hukumomin jihar nan 27.

A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a mayankar dabbobi ta Dutse, gwamnan jiha, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce hakan na daga cikin kudirin gwamnatin jiha na tallafawa ‘yan kungiyar domin su ji dadin gudanar da ayyukan su.

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin kwamishinan kananan hukumomi, Alhaji Kabiru Hassan Sugungun, ya ce gwamnati ta sahalewa shugabannin kananan hukumomi, su duba bukatun yan kungiyar da suka hadar da gyaran mayankar dabbobi na kananan hukumomi, tare da gina musu wasu sabbi da kuma gabatar da rahotan ga gwamnati.

Ya kuma basu tabbacin samar musu da hanyoyin dogaro da kai domin inganta rayuwarsu.

A jawabinsa na godiya, shugaban kungiyar mahauta na jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Mai-Doki ya bayar da tabbacin hadin kai da goyan bayan ‘yan kungiyar na cigaba da marawa manufofi da tsare-tsaren gwamnati baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: