Labarai

Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanar da ranar Asabar mai zuwa a matsayin ranar jarabawar tantancewa ga wadanda suka nemi tallafin karatu kyauta a jami’ar Al-Istiqama

Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanar da ranar Asabar mai zuwa 17 ga wata a matsayin ranar jarabawar tantancewa ga wadanda suka nemi tallafin karatu kyauta a jami’ar Al-Istiqama dake Sumaila a jihar Kano domin karatun digiri akan aikin jinya wato Nursing.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jiha, Dr. Salisu Mu’azu, wacce aka rabawa manema labarai a Dutse.

Sanarwar tace za ayi jarabawar tantancewar ne a kwalejin fasaha ta Jigawa dake Dutse da misalin karfe 11 na safe.

Babban sakataren yace daliban za su zo da sakamakon jarabawar kammala sakandire da na jarabawar JAMB ta bana da shaidar zama dan asalin karamar hukumar da kuma takardar haihuwa.

Ya kara da cewa idan suka iso makarantar, daliban za su duba dakin jarabawar karamar hukumarsu, wanda aka kafe a allon sanarwa a kofar shiga makarantar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: