Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da sauke sakatarorin kananan hukumomi 25 daga cikin 27

0 84

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da sauke sakatarorin kananan hukumomi 25 daga cikin 27 da jihar ke da su.

Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta jihar, Alhaji Najib Umar ne ya sanar da hakan yau Laraba a Dutse.

“Gwamnatin jihar Jigawa na sanar da cewa, ta sauke dukkanin sakatarorin kananan hukumomi 27 daga aikinsu, band ana kananan hukumomin Sule Tankarkar da Buji.

“An umarci sakatarorin da abin ya shafa da su mika dukkan kayan aikin ofisoshinsu da sauran kayayyaki ga Daraktocin Mulki nan take,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa, Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya godewa sakatarorin da aka cire bisa gagarumar gudunmawar da suka bayar wajen bunkasa kananan hukumomin da sukai aiki.

Sanarwar dai ta kuma ce, gwamnan ya yi musu fatan samun nasara a al’amuran da za su gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: