Gwamnatin jihar Jigawa ta ta biya Naira miliyan 79, da dubu 365 a matsayin kudin rajistar makarantun lauya ga yan jihar jigawa 181

0 81

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce ta biya Naira miliyan 79, da dubu 365 a matsayin kudin rajistar makarantun lauya ga yan jihar jigawa 181 da ke karatu a makarantun shari’a daban-daban na kasar nan a matsayin kudaden karfafa gwiwa.

Sakataren zartarwa na riko na kungiyar bayar da tallafin karatu ta jihar jigawa, Alhaji Saidu Magaji ne, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa jiya.

Ya ce a karkashin kyautar bursary hukumar ta kuma biya kudaden da suka kai Naira miliyan 3, da dubu dari 620 a matsayin alawus-alawus din su na yau da kullum.

Ya bayyana cewa gwamnati ta damu matuka da karancin malamai mata a fannin tattalin arziki a cikin gida.

Tare da daukar nauyin mata da dama don yin kwas a kwalejin kimiyya da fasaha ta Hussein Adamu da ke Kazaure.

Sun kuma dauki nauyinsu ne a karkashin shirin bunkasa malamai mata a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Bichi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: