Gwamnatin jihar jigawa tace kananan yara kusan dubu 200 za a baiwa maganin inganta garkuwar jiki domin rage yawan mace macen kananan yara

0 69

Gwamnatin jihar jigawa tace kananan yara kusan dubu 200 za a baiwa maganin inganta garkuwar jiki domin rage yawan mace macen kananan yara a fadin jihar nan.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ne ya sanar da hakan a wajen bikin kaddamar da shirin rabon maganin a cibiyar lafiya matakin farko ta garin Kudai dake karamar hukumar Dutse.

Gwamnan wanda ya sami wakilcin babban sakataren ma’aikatar lafiya, Dr Salisu Mu’azu, yace kananan yara yan wata daya zuwa watanni 11 ne za a baiwa maganin.

Ya kara da cewa shirin hadin gwiwa ne da ma’aikatar lafiya ta jiha da kuma kungiyoyin lafiya daban-daban da ba na gwamnati ba.

Yace kaddamar da rabon maganin a jihar Jigawa zai taimaka matuka wajen rage kamuwar yara daga cututtuka musa alaka da nimoniya da ciwon ido da kuma saura cututtuka masu halaka kananan yara.

Dr Salisu Mu’azu yayi kira ga iyeyen yara da su ba da muhimmanci wajen karbar maganin domin samun nasarar da ake bukata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: