Gwamnatin Jihar Jigawa tace nan ba da dadewa za ta sake bibiyar kundin tsarin cigaban jihar.

Kundin na kunshe da kudirorin gwmanati dake samar da cigaban jama’a da na tattalin arziki a matsakaici da dogon zango.

Wata sanarwa daga babban mai taimakawa gwamnan akan jaridu, Ahmad Muhammad Danyaro, tace Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya sanar da haka a jiya a lokacin da yake tattaunawa da ofishin cigaban kasashe na birtaniya domin fahimtar juna da huldar cigaba a Dutse.

A cewar Gwamnan, gwamnatin jihar na shirin samar da kundin cigaba mai ma’ana wanda zai shafi kowa da kowa domin tabbatar da cewa ta biyawa mutanen jihar Jigawa bukatunsu.

Daraktan ofishin cigaban kasashe na birtaniya, Dr. Christoper Pycroft ya yabawa jihar Jigawa bisa jajircewarta wajen zama kan gaba a bangaren cigaba mai ma’ana a yankin Arewa maso Yamma.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: