Gwamnatin Jihar Jigawa tare da hadin gwiwar gidauniyar Qatar da ta Mallam Inuwa zasu gudanar da aiyukan samar da ruwansha

0 76

Gwamnatin Jihar Jigawa tare da hadin gwiwar gidauniyar Qatar charity foundation da kuma gidauniyar Mallam Inuwa zasu gudanar da aiyukan samar da tashoshin samarda ruwansha masu amfani da hasken rana da tona rijiyoyin burtsatse da tuka tuka da kuma gina masalatai a wasu garuruwa na kananan hukumomin 27 na Jihar nan.

Hakan ya biyo bayan wani taro da bangarorin uku suka gudanar a birnin tarayya Abuja.

Inda taron ya tattauna hanyoyin da za a bi wajen samun saukin gudanar da aiyukan domin amfanin miliyoyin alummar jihar Jigawa.

Gwamnatin jihar Jigawa da gidauniyar Mallam Inuwa ce zasu sa ido akan yadda za a gudanar da aiyukan.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana jin dadinsa na gudanar da aiyukan na hadin gwiwa da gwamnatinsa tare da alkawarin samarda fili domin gudanar da aiyukan.

A nasa jawabin Daraktan cibiyar gidauniyar Qatar a Nigeria Mr Hamdi Elsayed yace gidauniyar ce zata gudanar da aikin kai tsaye tare da tallafin alummar kasar Qatar inda yace zasu tallafawa jihar Jigawa a fannin noman zamani

Leave a Reply

%d bloggers like this: