Gwamnatin jihar Jigawa za ta gina tsangayar koyon likitanci a jami’ar Sule Lamido dake Kafin Hausa

0 102

Daga: Kabiru Zubairu

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar ya bayyana cewa, shirye-shirye sun kammala domin fara gina tsangayar koyon likitanci a jami’ar jihar ta Sule Lamido University da ke Kafin Hausa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar lokacin da yake gabatar da kudirin kasafin kudi na shekarar 2022 ga majalissar dokokin jihar a ranar Laraba.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa ana samun cigaba a bangaren ilimi a jihar inda aka samu karin makarantun gwamnatin tarayya guda uku a jihar, yayin da a bangare guda kuma aka samu amincewa kan wasu kwasakwasai har sama da ashirin da biyar a manyan makarantun jihar.

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na yin duk mai yiwuwa wajen ganin an kara samun amincewa kan wasu kwasakwasan a manyan makarantun.

Badaru ya kuma ce, a shekarar da ake ciki gwamnati ta kashe Naira Biliyan 13.68 wajen fara aiyuka a sassa daban-daban na ilimi, wanda hakan na daya daga cikin kokarin gwamnatin na tabbatar da kudirinta na rage cunkoso a ajuzuwa da makarantu.

A shekarar 2022, Gwamnan ya bayyana cewa za a kashe Naira Biliyan 1.62 wajen biyan tallafin karatu ga dalibai masu karatu a Najeriya da kuma kasashen waje, ciki kuwa har da dalibai 160 da a kwanan nan aka tura kasar Sudan domin karatun likitanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: