Gwamnatin Jihar Jigawa zata fara tantance Ma’aikatan gwamnati da yan Fansho.

0 90

Gwamnatin Jihar Jigawa zata fara tantance Ma’aikatan gwamnati da yan Fansho daga ranar Laraba 16 ga watan Yunin da muke ciki.

Shugaban Ma’aikata na Jiha Alhaji Hussaini Ali Kila, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Ofishinsa Ibrahim Dutse Ibrahim, ya rabawa manema labarai a Dutse.

Sanarwar ta ce Manufar gudanar da tantancewar shine, domin a tabbatar da yawan Ma’aikatan da gwamnatin jiha take bawa Albashi, da kuma yan Fansho tsawon shekaru.

Shugaban Ma’aikatan Jiha, ya ce tantancewar zata bawa Ma’aikatan da suke da matsalar Albashi damar gwamnati ta gyara musu, sai dai ana bukatar su gabatar da Lambar Tantance Bankin su wato BVN, da sauran Abubuwan da ake bukata.

Haka kuma, sanarwar ta ce tantancewar ta kunshi Ma’aikatan Majalisar Dokoki, da Shari’a da kuma Ma’aikatan da suke aiki a Majalisar Masarautu na Jiha.

Kazalika, sanarwar ta ce daga cikin wuraren da Gwamnati ta ware domin tantancewar sun kunshi Sakatariya ta Jiha dake Dutse, da Ofishin hukumomin gwamnati, da hukumar SUBEB, da kuma Ofishin Sakatariyar Mulki ta Kananan hukumomi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: