Shugaban kwamitin bada rancen noma na maaikata kuma shugaban ma’aikata na jiha, Alhaji Muhammad K Dagaceri ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse.
Ya ce a yau Litinin 15 ga wata ne, Gwamna Umar Namadi zai kaddamar da shirin bada rancen a hedikwatar kamfanin samar da kayayyakin amfanin gona na jihar Jigawa JASCO da misalin karfe goma sha daya na safe.
Alhaji Muhammad Dagaceri ya kara da cewar baya ga maaikata, masu rike da mukaman siyasa da suka hadar da sakataren gwamnati da kwamishinoni da masu bada shawara da mataimaka na musamman da shugabannin hukumomin gwamnati da yan majalissar dokoki ta jiha da alkalai zasu amfana da shirin
Ya cigaba da cewar za a bada bashin ne domin yin noman shinkafa da Gero da Dawa da kuma Ridi
Shugaban maaikatan ya ce an zabo maaikata dubu goma sha hudu daga cikin dubu hamsin da bakwai da dari shida da ake dasu domin cin gajiyar shirin a karon farko.
Bashin, ya kunshi taki da magungunan feshi da kuma kudin barema naira dubu dari biyar da kuma naira dubu dari biyu da hamsin, wanda za a biya a tsawon shekara guda.