Gwamnatin Jihar Kaduna ta fara janye takunkumin da ta sanyawa makarantun data rufe saboda karya dokokin yaki da cutar Corona kimanin shekara guda

0 67

Gwamnatin Jihar Kaduna a jiya ta janye takunkumin da ta sanyawa Makarantar Future Leaders International School wanda take Unguwan Rimi a birnin Kaduna, saboda karya dokokin yaki da cutar Corona kimanin shekara 1 da watanni 5 kenan.

Babban Sakatare a Ma’aikatar ilimi ta Jihar Kaduna Alhaji Yusuf Saleh, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya.

Alhaji Saleh ya ce gwamnati ta cire takunkumin da ta sanyawa makarantar domin cigaba da aiki.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa an rufe Makarantar ne saboda samun su da bada izinin rubuta Jarabawar shiga Karamar Sikandire da babban Sikandire, inda aka ta a ranar 11 ga watan Yuni na shekarar 2020.

Kwamishinan Ilimi na Jihar Alhaji Shehu Makarfi, ya ce an rufe makarantar ne saboda samun su da laifin karya dokar a rufe makarantu kamar yadda gwamnatin jihar ta umarta.

Kazalika, ya ce bayan dogon Nazari Gwamnatin Jihar Kaduna, ya amince makarantar ta cigaba da karatu daga ranar 8 ga watan Nuwambar da muke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: