Gwamnatin Jihar Kaduna ta roki mutanen jihar da su kauracewa yunkurin daukar fansar kashe-kashe

0 86

Gwamnatin Jihar Kaduna a yau ta roki mutanen jihar da su kauracewa yunkurin daukar fansar kashe-kashe.

An samu yawaitar kashe-kashen mutane da na ramuwar gayya cikin watannin da suka gabata a jihar, lamarin da hukumomin tsaro suka kasa dakilewa.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya nakalto mai rike da mukamin gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe na yin rokon.

A cikin wata sanarwa da aka fitar jiya, Samuel Aruwan yace rokon ya biyo bayan kisan mutane 3 a yankin karamar hukumar Zangon Kataf a jihar.

Yace an bayar da rahoton kisan mutane ukun a wani hari na wasu mutane da ba a gano ko su waye ba, wadanda suka mamaye wasu kauyuka a yankin karamar hukumar Zangon Kataf.

Samuel Aruwan yace an raunata mazauna kauyukan su 4 yayin da aka lalata wata mota 1 da gidaje uku da bukkoki 8.

Leave a Reply

%d bloggers like this: