Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da kashe wasu yan bindiga da dama bayan sojoji sun kaiwa sansanin su hari a kananan Hukumomin Igabi da Chikun na Jihar

0 69

Gwamnatin Jihar Kaduna, ta tabbatar da kashe wasu yan Bindiga da dama, bayan Sojoji sun kaiwa sansanin su hari a kananan Hukumomin Igabi da Chikun na Jihar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Mista Samuel Aruwan, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jiya.

A cewarsa, Sojojin suna cigaba da kakkabe yan bindigar da sauran batagari a wurare daban-daban na Jihar musamman a Kananan Hukumomin Chikun da Igabi, inda suka kashe yan ta’addar da dama tare wasu kuma suka tsere da harbin bindigogi a Jikinsu.

Mista Aruwan, ya ce Sojojin sun lalata sansanin yan bindigar na Apewohe da ke karamar hukumar Chikun gaba dayan sa.

Haka kuma ya ce Sojojin sun lalata wasu daga cikin Maboyar yan bindigar a garuruwan Dakwala da Kunai duk cikin karamar hukumar ta Chikun.

Kwamishinan, ya kuma ce Sojojin sun yi nasarar kubutar da mutane 10 wanda yan bindigar suka yi garkuwa da su, inda suka daure su da Sarka.

Da ya ke bayyana farin cikin sa, Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasiru El-Rufa’i ya yabawa Sojojin bisa Nasarar da suka samu na kubutar da mutane 10.

Leave a Reply

%d bloggers like this: