Gwamnatin Jihar Kaduna a jiya ta tabbatar da kisan mutane 12 tare da raunata 2, a wani hari da akai a karamar hukumar Zangon Kataf ta Jihar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida Mista Samuel Aruwa, shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

Mista Aruwan ya ce hukumomin tsaro sun tabbatarwa da gwamnatin jihar cewa kimanin mutane 12 ne suka mutu, biyo bayan harin da wasu yan bindiga da suka kai a karamar hukumar.

Kwamishinan ya ce mutane 2 da suka samu raunika, suna cigaba da samun kulawar likitoci a Asibiti.

Sanarwar da Kwamishinan ya fitar ya ce Gwamna Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana Alhininsa kan kisan mutanen.

A cewarsa, Gwamnan ya jajantawa Iyalan wadanda aka kashe a yayin harin, tare da yiwa marasa lafiyar addua’ar samun sauki.

Kazalika, ya ce hukumomin tsaro suna cigaba da gudanar da sumame a yankin domin yin bincike.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: