Gwamnatin Jihar Kano ta yi wa dalibanta karin kashi 50 cikin 100 na kudaden tallafin karatu da take ba su

0 76

Gwamnatin Jihar Kano ta yi wa dalibai ’yan asalin jihar karin kashi 50 cikin 100 na kudaden tallafin karatu da take ba su.

Gwamnan Jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje, shine ya bayyana hakan a taron bikin cikar Najeriya shekaru 61 da samun yan cin kai, a birnin Kano.

Gwamnan wanda Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Malam Muhammad Garba ya wakilta, ya ce kwanan nan za’a fara biyan tallafin karatun.

A cewarsa, hakan yana cikin kudurin gwamnatin Jihar na bada Ilimi kyauta kuma Dole.

Gwamna Ganduje, ya bukaci Daliban su yi amfani da damar da aka basu wajen tabbatar da cewa sun inganta karatun su.

Da yake magana kan cigaba da aikin rijistar Katin Zabe, Gwamnan ya bukaci Daliban su tabbatar sun samu katin su domin kada kuri’un su.

Tun farko a jawabinsa, Dr Saidu Ahmed Dukawa na Sashen Nazarin Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Bayero dake Kano, ya bukaci yan Siyasa su mayar da hankali kan gina kasar nan domin ciyar da ita gaba. 

Leave a Reply

%d bloggers like this: