Gwamnatin jihar Kano tana bawa alhazan jihar dake kasa mai tsarki abinci kyauta sau biyu a kullum

0 153

Gwamnatin jihar Kano ta ce tana baiwa alhazan jihar da a halin yanzu suke kasar Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin bana na 2024 abinci kyauta sau biyu a kullum.

Shugaban tawagar yada labarai na alhazan jihar Kano kuma mai magana da yawun mataimakin gwamnan jihar Shuaibu Ibrahim ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau.

Baya ga abincin, gwamnatin jihar Kano ta kuma tura tawagar kwararrun likitoci zuwa kasar Saudiyya domin kula da alhazan.

Bugu da kari, gwamnatin jihar ta kuma tura tawagar kula da muhalli domin tabbatar da tsaro da tsaftar muhallin mahajjata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: