Gwamnatin jihar Kano za ta karbo bashin naira biliyan 4 da don kammala ayyukan samar da wutar lantarki

0 120

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da karbo bashin naira biliyan 4 da gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta nema don kammala ayyukan madatsun ruwa Tiga da Challawa domin samar da lantarki.

An bayar da wannan amincewar ne a zaman da shugaban majalisar Hon Hamisu Ibrahim Chidari ya jagoranta.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na Majalisar, Uba Abdullahi ya fitar, wanda ya ce majalisar ta tattauna kan lamarin bayan kakakin majalisar ya karanta wasikar da gwamnan ya aika wa majalisar.

A cewarsa, shugaban masu rinjaye ya yi kira ga majalisar da ta duba wannan bukata sannan ta bayar da damar ciyo bashin, wanda ya ce yana da fa’ida mai yawa ga jama’ar jihar.

Hakazalika, yayin zaman majalisar, dokar kula da yawon bude ido ta jihar Kano ta bana ta tsallake karatu na uku bayan kwamitin ya duba sassan dokar kuma ya yi gyare-gyare yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: