Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da umarnin dawo da kafar sadarwa ta waya a kananan Hukumomi 13

0 43

Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da umarnin dawo da kafar sadarwa ta waya a kananan Hukumomi 13 wadanda rikin ta’addanci ya shafi.

Mai bai wa gwamna Aminu Masari shawara na musamman akan harkokin tsaro, Alhaji Ibrahim Katsina, ya tabbatar da haka ga kamfanin dillancin labarai na kasa jiya a Katsina.

Yace umarnin ya biyo bayan kwarkwaryar zaman lafiyar da aka samu a kananan hukumomin da abin ya shafa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya tunatar da cewa gwamnatin jihar a watan Satumba ta bayar da umarnin katse kafar sadarwa ta waya a kananan Hukumomi 13 da ‘yan fashin daji suka addaba.

Kananan hukumomin sune Jibia, Batsari, Safana, Kurfi, Danmusa, Dutsin-Ma, Kankara, Matazu, Musawa, Funtua, Faskari, Sabuwa, Dandume, Bakori, Danja da Malumfashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: