Gwamnatin jihar Neja ta sanar da bullar cutar murar tsuntsaye a cikin wasu gidajen kiwon kaji da ke jihar.

Jami’in yada labarai na Ma’aikatar Kiwon Dabbobi, Abubakar Kuta, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a yau a Minna, babban birnin jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa kaji a jihar na kamuwa da cutar murar samnfurin A

Sanarwar ta bayyana cewa an yi asarar dubban tsuntsaye a jihar, na miliyoyin nairori, sanadiyyar cutar murar.

Ta shawarci masu kiwon kaji da su kiyaye kuma su kai rahoton duk wani abin da ya faru na yawan mutuwar tsuntsayensu ga ma’aikatar. Sanarwar ta shawarci manoma su kula da tsaftar gona, tare da takaita zirga-zirgar ababen hawa da mutane dake zuwa gonakinsu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: