Gwamnatin jihar Neja ta yi kira ga hukumar kula da shige da fice ta kasa immigration da ta taimaka wajen duba kwararar bakin haure cikin jihar a wani mataki na kokarin magance rashin tsaro.

Sakataren gwamnatin jihar Ahmed Ibrahim Matane ne ya yi wannan roko a lokacin da sabon kwanturolan immigration na jihar Nongo Samuel Shima ya kai masa ziyara.

A wani lamari makamancin wannan, ‘yan bindiga sun kai farmaki a kauyukan gundumar Bashar da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato.

Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan ya shaidawa manema labarai cewa dagatan kauyukan da wasu mazauna kauyukan sun tsere.

Wani mazaunin kauyukan shima ya shaida wa manema labarai cewa suma suna shirin tserewa saboda masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyukan kuma suna kai musu farmaki a kowace rana.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba akan lamarin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: