Gwamnatin jihar Zamfara ta ce an kama sama da mutane dubu 2 da ake zargi da yiwa ‘yan fashin daji leken asiri

0 69

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce an kama sama da mutane dubu 2 da ake zargi da yiwa ‘yan fashin daji leken asiri, tun daga lokacin da ta katse hanyoyin sadarwa da fara kai farmakin sojoji a jihar.

Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan a yau yayin wani taro da manema labarai a Kaduna.

Ibrahim Dosara ya ce wadanda aka kama, sun bayar da muhimman bayanai kan ayyukansu da kuma yadda ake zargin wasu manyan mutane ne suke daukar nauyinsu.

Ya ce an samu nasarar ayyukan tsaro a jihar, inda ya kara da cewa ‘yan bindiga da yawa sun tsere daga jihar kuma sauran na fama da yunwar da ta tilasta musu cin danyen abinci sakamakon takunkumin da gwamnati ta kakaba musu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: