Gwamnatin kasar Habasha ta ce babu gudu ba ja da baya wajen ci gaba da yaki da dakarun ‘yan tawayen Tigray

0 119

Gwamnatin kasar Habasha ta ce babu gudu ba ja da baya, wajen ci gaba da yaki da dakarun ‘yan tawayen Tigray, duk da kiran da kasashen duniya ke ci gaba da yi na a yayyafawa zukata ruwa.

Wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta ce Habasha ba za ta taba bayar da kai ga farfagandar kasashen waje ba.

Yayin da gwamnati ke cewa tana gab da samun nasara, yan tawayen na Tigray da ke ci gaba da tunkarar babban birnin kasar bayan kwace wasu muhimman garuruwa, suma sun ce ba sulhu.

Kilomita 300 ne kacal ya rage tsakanin dakarun yan tawayen da birnin Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Kasashen Afirka, da Tarayyar Turai da Amurka dai na sake yin kira da a sasanta don kawo karshen rikicin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: