‘Gwamnatin mu zata cigaba da mayar da hankali wajen samar da rayuwa mai inganci ga yan Najeriya’ -Osinbajo

0 81

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yace gwamnati mai ci ta mayar da hankali wajen samar da rayuwa mai inganci ga dukkanin ‘yan Najeriya daidai lokacin da kasarnan ke samun cigaba duk da tarun kalubalen da ake fuskanta.

Yayi magana a jiya wajen yaye manyan ma’aikatan gwamnati da suka yi karatu a makarantar horas da manyan ma’aikata dake Kuru a kusa da Jos, babban birnin jihar Filato.

Mataimakin shugaban kasar, wanda ya samu wakilcin babban hafsan tsaro, Janar Lucky Irabor, yace a zaune take cewa an sha wahala tare da kashe kudade wajen samar da tsaro da kuma inganta yanayin rayuwar dukkan ‘yan Najeriya.

Yemi Osinbajo ya bukaci dukkan manyan ma’aikatan da suka yi karatun da su bawa marada kunya ta hanyar fitar da hanyoyi masu kyau da bayar da shawarwari wajen aiwatar da ayyukan da zasu taimakawa kasarnan wajan shawo kan matsalolin da suka shafi raunin mulki da kalubalen da suke haifarwa akan ayyukan gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: