Gwamnatin Najeriya ta ce a a kwaso ƴan ƙasarta da ke kasar Ukraine saboda tashin hankali

0 73

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa a shirye take ta kwashe ƴan ƙasarta da ke son barin Ukraine bayan Rasha ta kutsa ƙasar.

A wata sanarwa da gwamnatin Najeriyar ta fitar ta hannun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, ta ce ta yi mamaki kan harin da Rasha ta kai ƙasar.

Wata mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Francisca Omayuli ta bayyana cewa ofishin jakadancin Najeriya a Ukraine ya tabbatar mata da cewa ƴan Najeriya da ke Ukraine za su kasance cikin tsaro kuma ana ɗaukar matakai na kwashe waɗanda suke so su bar ƙasar

Leave a Reply

%d bloggers like this: