Gwamnatin Najeriya ta nuna rashin yarda da yadda ake yi wa ƴan ƙasarta wariya da ke neman ficewa daga kasar Ukraine

0 169

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda rahotanni suka nuna ana nuna wa wasu ƴan Najeriya wariya da ke yunkurin ficewa daga kasar Ukraine.

Kimanin ‘yan Najeriya 4,000 ne har yanzu ke maƙale a Ukraine.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a Twitter, ta ce jami’an tsaro da ‘yan sandan Ukraine sun ƙi barin ƴan Najeriya su shiga bas da jiragen kasa da ke kan iyakar Ukraine da Poland.

“Wanirukuni na ɗaliban Najeriya da aka hana su shiga ƙasar Poland sun yanke shawarar cewa ba su da wani zabi illa su sake ratsa Ukraine domin yunkurin ficewa daga ƙasar ta kan iyakar kasar da Hungary,” in ji sanarwar.

Ofishin Buhari ya ce ya kamata a mutunta duk ƴan kasashen waje da ke koƙarin tsallakawa zuwa kasar Poland ba tare da nuna bambanci ba.

Sanarwar ta ce “Duk waɗanda suka guje wa wani rikici na da ‘yancin shiga cikin aminci a karkashin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kuma bai kamata a nuna bambanci ba kan fasfo dinsu ko launin ba.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: