Gwamnatin Najeriya ta shigar da ƙarar Sanata Natasha kan zargin ƙage da ta yi a gidan talabijin kai-tsaye
Gwamnatin tarayya ta shigar da ƙarar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, saboda zargin ɓata suna da ta yi a gidan talabijin kai-tsaye.
Gwamnatin na zargin dakatacciyar ƴarmajalisar, da ”yin ƙage, duka kuwa da ta san cewa hakan zai shafi ƙimar mutum”, tana mai kafa hujja da cewa yin hakan laifi ne da ke ɗauke da hukunci ƙarƙarshin sashe na 392 na kundin tsarin mulkin ƙasar.
Daga cikin jerin mutanen da gwamnatin da sanya a matsayin shaidun da za su tabbatar da zargin, har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.
Ɗaya ɗaga cikin tuhume-tuhumen da gamnatin ke yi wa Sanata Natasha shi ne inda ta zargi Godswill Akpabio da Yahaya Bello da yunƙurin kitsa kasheta. A farkon watan Maris ne da Majalisar Dattawan Najeriyar ta dakatar da sanatar har na tsawon wata shida bisa shawarwarin da kwamitin Ɗa’a da Ladabtarwa da Sauraron ƙorafin Jama’a na majalisar ya bayar, bayan nazari kan ƙorafin da Sanata Natasha ta miƙa wa majalisar.