A ranar Litinin ne gwamnatin Sudan ta Kudu ta aike da ƙarin sojoji 300 zuwa makwaɓciyarta Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a karkashin haɗakar kungiyar ƙasashen yankin.
Za su kasance cikin dakarun yankin gabashin Afirka da ke yaki da kungiyar ‘yan tawayen M23.
Hakan ya kawo adadin sojojin Sudan ta Kudu sama da 1,000 a ƙasar, a cewar ministan tsaron ƙasar, Janar Chol Thon Balok.
Za a tura sojoji ne zuwa Goma – hedkwatar sojojin yankin. Za a maye gurbinsu bayan shekara ɗaya.
Sudan ta Kudu ita ce ƙasa ta baya-bayan nan da ta shiga cikin rundunar ƙasashe bakwai da aka kafa a watan Yunin shekarar da ta gabata domin tabbatar da zaman lafiya a gabashin Kongo.
- Comments
- Facebook Comments