Gwamnatin Kafar Sudan ta tabbatar da yunkurin yin juyin mulki a kasar.

Rahotanni daga babban birnin kasar Sudan Khartoum da kuma Omdurman na cewa an baza sojoji a kan titi an kuma rufe gadojin da ke mahadar kogin Nil.

Jaridar AFP ta ambato majiyar gwamnati na cewa makitsan juyin mulkin sun yi kokarin kwace ginin gidan talabijin na kasar.

Kazalika hotunan da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna tankokin yaki na yawo a kan manyan tituna.

Hukumomin Sudan sun ce suna kan daukar matakan dai-daituwar al’amura a kasar.

Kamar yadda jaridar Reuters ta ruwaito kakakin gwamnati Mohamed Al Faki na cewa, ba da jimawa ba za a fara binciken wadanda ake zargi da kitsa juyin mulkin.

Shekaru biyu da suka wuce ne a ka kifar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar Albashir, sannan a ka kafa gwamnatin riko da ta kunshi sojoji da fararen hula.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: