Gwamnatin Syria ta yanke hukuncin kisan kan mutane 24 bisa samun sa da laifin kunna wutar daji

0 209

Gwamnatin Syria ta yanke hukuncin kisan kan mutane 24 bisa samun sa da laifin kunna wutar Daji wanda aka samu a shekarar da ta gabata.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Shari’ah ta Kasar ta rabawa manema labarai, inda ta ce wutar da mutanen suka kunna ta yi sanadiyar janyo asarar rayuka da kuma lalacewa gine-ginen gwamnati.

Sanarwar ta ce an kuma yankewa wasu 11 hukuncin daurin gidan Yari da aiki mai tsanani tsawon rayuwarsu, da wasu 5 wanda zasu aiki bisa gidan Yarin na tsawon shekaru 10 zuwa 20 saboda zarge-zargen da ake musu.

Kawo yanzu ba’a bayyana kamannin mutanen da kuma sunayen su ba, da kuma ranar da za’a zartar musu da hukuncin.

Wani rahoto ya yi nuni da cewa sanadiyar faruwar lamarin, kimanin Gobara 187 suka haifar, wanda suka suka shafi garuruwa 280 cikin shekarar da ta gabata.

A kalla mutane 3 ne suka mutu 12 kuma suka samu raunika, akmar yadda kafafen yada labarai na JIhar suka rawaito.

Leave a Reply

%d bloggers like this: