Gwamnatin tarayya bata da bukatar ambaton sunaye da kunyata wadanda suke daukar nauyin ta’addanci

0 67

Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina, yace gwamnatin tarayya bata da bukatar ambaton sunaye da kunyata wadanda suke daukar nauyin ta’addanci.

Femi Adesina, wanda ya sanar da haka a jiya, yayin wata fira a gidan talabijin na Channels, yace gwamnati ta fi mayar da hankali wajen tabbatar da cewa an hukunta wadanda aka kama da laifi.

Yana mayar da martani ne akan batutuwan da watakila shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tattauna akai a wajen babban taron majalisar dinkin duniya.

A kan haka, aka tambayi hadimin shugaban kasar ko shugaban kasar zai yi magana kan matakin hadaddiyar daular larabawa na ayyana neman ‘yan Najeriya 6 ruwa a jallo saboda hannu a ta’addanci.

‘Yan Najeriyan 6 suna daga cikin 38 wadanda daular ta labarawa ke zargin suna daukar nauyin ta’addanci.

Amma da yake bayar da amsa, Femi Adesina, yace gwamnati baza ta ambaci sunayen mutanen domin kunyata su ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: