Ministan Matasa da Cigaban Wasanni Sunday Dare, ya ce gwamnatin tarayya na shirin samar da asusun zuba jari na matasa na kasa don zama bankunan matasa.

Ya bayyana haka ne a jiya Alhamis yayin da yake gabatar da jawabi a taron karawa juna sani na ministoci karo na 51 da kungiyar sadarwar fadar shugaban kasa ta shirya a fadar shugaban kasa, dake Abuja.

Ya ce da zarar Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da bukatar kafa bankunan matasa, shirin zai magance matsalar karancin kudi da lamuni da kuma karancin sana’o’i a tsakanin matasa, ta yadda za a ba su damar cimma burinsu.

Sunday Dare, wanda ya ce dalilin da ya sa wannan shirin shi ne sanin cewa sana’o’i shi ne jigon ci gaban matasa.

Ministan ya ce kawo yanzu sama da matasa dubu 31 ne suka ci gajiyar asusun zuba jari na matasa na kasa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: