Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon shirin Zuba Jari a fannin Sauyin Yanayi wato NCIP

0 96

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani sabon shirin Zuba Jari a fannin Sauyin Yanayi wato NCIP, domin buɗe ƙofofin fitar dakuɗaɗen kare muhalli da kuma haɓaka ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa. An tsara shirin ne domin tara kuɗaɗe har dala miliyan 500 don aiwatar da muhimman ayyuka na gina ababen more rayuwa da kuma jure sauyin yanayi a faɗin ƙasar.

An ƙaddamar da wannan shirin ne bayan wani babban taro da aka gudanar a Abuja tsakanin Ministan Kuɗi kuma Ministan Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Mista Wale Edun, da jami’an Hukumar Zuba Jari ta Ƙasa (NSIA), Hukumar Sauyin Yanayi (NCCC), da kuma wakilan Asusun Kare Muhalli na Duniya (GCF). Ma’aikatar Kuɗi ce ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar yau.

A yayin taron, Minista Edun ya bayyana cewa Hukumar Zuba Jari ta Ƙasa na da kwarewa da amincewa wajen jagorantar shirin. Ya ce akwai buƙatar Najeriya ta ci gajiyar damar da ke cikin kuɗaɗen kare muhalli domin farfaɗo da tattalin arziki, tallafa wa noma, bunƙasa fasahar zamani da kuma inganta fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje. Shima Daraktan Hukumar Zuba Jari ta Ƙasa, Aminu Umar-Sadiq, ya bayyana cewa an ƙirƙiri wannan shiri ne domin jawo hankalin masu zuba jari daga cikin gida da waje. A nata bangaren, Daraktar Hukumar Sauyin Yanayi, Dokta Nkiruka Maduekwe, ta ja hankalin gwamnati da ta hanzarta ƙara samun damar shiga asusun kare muhalli na duniya, tana mai cewa ƙasashe ƙanana ma sun fi Najeriya yawan hukumomin da aka amince da su a wannan fanni.

Leave a Reply