Gwamnatin tarayya ta amince da bada kudi naira 309.9 domin gina titina wanda aka baiwa kamfanin Dangote kwangilar

0 82

Gwamnatin tarayya ta amince da bada kudi kimanin naira 309.9 domin gina titina  wanda aka baiwa kamfanin dangote kwangilar gina su.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola shine ya bayyana hakan ga manema labarai bayyan sun kammala tattaunawa da hukumomin tarayya dangane da aikin titin guda biyar na kimanin kilomitici 274.9 na hanyoyin gwamnatin tarayya.

Hanyaoyin za’ayi sune tsakanin garin Bama da Banke a jihar Borno,da kuma titin Nnamdi Azikiwe a garin kaduna da kuma wasu hanyoyin guda uku a garin lagos da suka hada hanyar Epe zuwa Sagamu.

Mista Fashola ya bayyana cewa wadannan manyan ayyukan na daga cikin wanda gwamnatin tarayya ta sahalle ayi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: