Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Litini da Talata a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Babbar Sallah

0 75

Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranakun Litinin 11 da Talata 12 ga watan Yulin da muke ciki a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Babbar Sallah.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin ya taya daukacin al’ummar Musulmi da ‘yan Nijeriya na gida da kuma na kasashen waje murnar wannan rana.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar Shuaib Belgore, a ranar Alhamis, kuma aka rabawa manema labarai a Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: