Gwamnatin tarayya ta ba da umarnin cigaba da zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna daga ranar 23 ga watan Mayu

0 61

Gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar sufuri ta tarayya ta ba da umarnin ci gaba da zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna daga ranar 23 ga watan Mayu.

Kakakin hukumar kula da sufurin jiragen kasa Yakub Mahmood ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Legas.

Yakub Mahmood ya ce hukumar na son sanar da abokan huldar cewa an kara daukar matakan tsaro a tashoshi da titinan jiragen kasa domin tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji.

Ya ce irin wadannan matakan ba a titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna kadai aka dauka ba, har ma da dukkanin titinan jiragen kasa na fasinja, musamman sabbin titinan jiragen kasa.

Sawaba ta ruwaito cewa, a ranar 28 ga watan Maris ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai hari kan wani jirgin kasa da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda aka kashe akalla mutane takwas tare dayin garkuwa da wasu ko suka bata.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa a ranar 29 ga watan Maris ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna har zuwa wani lokaci bayan harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: