Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shirya-shiryen inganta albashin malaman makaranta na dab da kammaluwa

0 106

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa shirya-shiryen inganta albashin malaman makaranta da kuma yayayin ayyukansu.

Karamin ministan ilimi Chukwuemeka Uwajiuba, ya bayyana haka jiya Alhamis a birnin Benin yayin bikin yaye wanda suka kammala samun horon koyarwa da aka gudanar.

Yayin da babban mai bashi shawara Misis Muna Onuzo-Adetona ta wakilce shi a taron, yace gwamnati mai ci zata cigaba da yin duk mai yuwa wajen bunkasa harkokin ilimin kasar nan tare da warware duk wasu matsaloli da ka iya kawo tazgaro a tsarin koyarwa.

Yayi bayanin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cigaba da aiki tukuru domin ganin yadda za’a inganta da sake fasalin tsarin koyarwa da zai yi dai-dai da zamani, musamman wajen samar da kwarrun Malamai domin gogayya da sauran kasashen da suka ci gaba a duniya.

A cewarsa gwamnatin tarayya ta bayyana malaman makarantu matsayin tubalin gini kasa, da haka ya amince kara musu wa’adin aiki daga kan shekara 60-65 da haihuwa, da kuma kara wa’adin aikin daga shakara 35-40.

Leave a Reply

%d bloggers like this: