Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin haɗin gwiwa da Jihar Jigawa domin ƙarfafa samar da sukari a ƙasar

0 171

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin haɗin gwiwa da Jihar Jigawa domin ƙarfafa samar da sukari a ƙasar nan da kuma cimma burin dogaro da kai a wannan fanni.

Wannan yunƙuri na cikin tsarin “Renewed Hope Agenda” na Shugaba Bola Tinubu, wanda ke da nufin inganta samar da abinci, ƙirƙirar ayyukan yi, da ba matasa dama domin bunƙasa tattalin arziki.

Ministan Albarkatun Ruwa da Tsabtar Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, ya sanar da hakan yayin wata ziyarar girmamawa da Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya kai masa a Abuja, inda ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin dabarar inganta rayuwar al’umma.

Farfesa Utsev ya ce zai kai ziyara ta aiki zuwa masana’antar sukari da ke jihar domin tantance yanayin samuwar ruwa da kuma gano wuraren da ma’aikatar za ta iya kawo gudummawa don tabbatar da ingantaccen aiki da amfanuwar al’umma, yayin da Gwamna Namadi ya ce manufar ziyarar ita ce neman goyon baya wajen tabbatar da samuwar ruwa mai ɗorewa ga masana’antar, wanda zai ƙara wa tattalin arziƙin jihar ƙima da taimakawa ci gaban ƙasa.

Leave a Reply