Gwamnatin tarayya ta ce dukkanin shirye-shirye sun kammala na bayar da kwangilar aikin hanyar Kano zuwa Gumel ta wuce zuwa Maigatari

0 79

Gwamnatin tarayya ta ce dukkanin shirye-shirye sun kammala na bayar da kwangilar aikin hanyar Kano zuwa Gumel ta wuce zuwa Maigatari.

Babban sakataren ma’aikatar ayyuka da gidaje na kasa, Babangida Hussaini ya bayyana haka lokacin bikin karbar aikin hanyar Shuwarin zuwa Azare da Shuwarin zuwa Dutse ta wuce zuwa Kwanar Huguma.

Ya ce haka kuma gwamnatin tarayya zata bada aikin gyaran kwanonin hanyar Kano zuwa Birnin Kudu domin rage ukuwar hadura.

Ya ce makwanni biyu da suka wuce gwamnatin ta mika aikin tituna masu yawa wadanda suka hada wasu jihohin kasarnan 4 a wani bangare na tabbatar da dorewar cigaban tattalin arziki.

Daga nan ya yabawa gwamna Muhammad Badaru Abubakar da yan majalisar kasa bisa kokarinsu na tabbatar da ganin an kammala aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: