Gwamnatin tarayya ta ce kawo yanzu ta kashe naira biliyan goma sha biyu wajen ciyar da daliban firamare a jihar Jigawa

0 85

Gwamnatin tarayya ta ce kawo yanzu ta kashe naira biliyan goma sha biyu wajen ciyar da daliban firamare a jihar Jigawa tun bayan bullo da shirin ciyar da abinci a gida a shekarar 2017.

Jami’in kula da shirin na jiha, Malam Nafi’u Halilu ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Fitila na mako-mako na Rediyo Jigawa.

Ya ce an biya Naira miliyan dari shida a duk wani kudin da aka biya masu dafa abinci a jihar.

Malam Nafi’u Halilu ya ce andauki masu dafa abinci dubu goma aiki a jihar jigawa.

Ya ce an bullo da shirin ne domin rage daliban da suka daina zuwa makaranta, samar da ayyukan yi, inganta tsaftar yara da inganta harkokin noma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: