Gwamnatin tarayya ta ce ta fara kin karɓar rigakafin cutar corona wanda suke da karamin wa’adi kafin su lalace

0 167

Gwamnatin tarayya ta ce ta fara kin karbar Rigakafin cutar Corona wanda suke da karamin wa’adi kafin su lalace ko kuma wanda baza suzo kasar nan akan lokacin ba.

Ministan Lafiya Dr Osagie Ehanire, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani kan wani rahoton da ke cewa kimanin alluran rigakafin Miliyan 1 ne suka lalace, biyo bayan karewar wa’adin su.

Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters, ya bayar da rahoton cewa wasu majiyoyi biyu sun bayyana masa cewa mafiya yawan rigakafin mallakin AstraZeneca ne wanda aka kawo su daga Nahiyar Turai.

Kamfanin ya bayyana cewa lalacewar Alluran suna daya daga cikin manyan Asarar da kasar nan tayi, ganin yadda Nahiyar Afrika take shan wahala wajen samun rigakafin.

Da yake bayar da martani cikin wata sanarwa, Ministan ya bayyana cewa Nijeriya ta samu nasarar Alkinta rigakafi Miliyan 10 da aka kawo kasar nan, wanda hakan ya sanya Najeriya ta samu Nasarar Alkinta Naira Biliyan 16 da Miliyan 400.

Kazalika, ya ce tun da farko gwamnatin tarayya ta cire Alluran, kuma hukumar Lura da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa NAFDAC, ce zata lalata su yadda ya kamata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: