Gwamnatin tarayya ta ce ta karbin kashi na karshe na jiragen yaki guda 12 samfurin Super Tucano da take tsammani daga Amurka

0 89

Gwamnatin tarayya ta ce ta karbin kashi na karshe na jiragen yaki guda 12 samfurin Super Tucano da take tsammani daga Amurka.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan a jiya lokacin da yayi magana ta cikin shirin kiran waya na TV Continental.

Ministan ya ce tare da nasarorin da sojoji suka samu a kan rashin tsaro, ya yi mamakin wani labari a jiya dake cewa rundunar sojin saman Najeriya ta biya kudi naira miliyan 20 a matsayin cin hanci ga ‘yan fashin daji don kada su harbo jirgin shugaban kasa.

Lai Mohammed ya ce tare da inganta yanayin tsaro a shiyyar Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya, kasarnan za ta fuskanci ingantuwar wadatar abinci.

Ministan ya bayar da tabbacin cewa za a cigaba da samun nasarar da sojojin ke yi kan ‘yan ta’adda da ‘yan fashi daji.

A saboda haka, ya nemi hadin kai da goyan bayan ‘yan Najeriya domin dorewar ayyukan sojojin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: