Gwamnatin Tarayya Ta Ce Za A Kammala Aikin Titin Kaduna-Zariya-Kano Kafin Ranar 29 Ga Watan Mayu

0 180

Gwamnatin tarayya ta ce za a kammala aikin titin Kaduna zuwa Zariya zuwa Kano kafin ranar 29 ga watan Mayu.

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji-Fashola ne ya bayyana haka a jiya yayin da ya kai ziyarar duba aikin babbar hanyar.

Bangaren babbar hanyar wani tsagi ne na aikin da ya kai kilomita 375.4 daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano da aka bayar a lokacin wa’adin mulkin Buhari na farko.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, an rarraba aikin sake gina titin Abuja zuwa Kaduna zuwa Zaria zuwa Kano zuwa kashi uku.

Babatunde Fashola ya ce yayin da aka kusa kammala kashi na biyu da na uku mai tsayin kilomita 210, za a bar sashe na daya daga Abuja zuwa Kaduna ga gwamnati mai jiran gado.

Babatunde Fashola ya bayyana cewa al’amuran da suka kawo tsaikon aikin sun hada da sauya matsugunin gine-gine, da na’urorin lantarki, da kasuwanni.

Leave a Reply