Gwamnatin Tarayya ta ce za ta ci gaba da karbar Harajin VAT ba kakkautawa

0 68

Gwamnatin Tarayya ta ce Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Kasa za ta ci gaba da karbar Harajin VAT bayan hukuncin Kotun daukaka kara kan lamarin.

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa hakan a birnin New York yayin da yake magana kan rashin jituwa bisa karbar harajin VAT tsakanin Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Kasa da Gwamnatin Jihar Ribas.

Babban lauyan tarayyar ya bayyana cewa hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na cewa a cigaba da zama kamar yadda ake tsakanin hukumar tara kudaden shiga ta kasa da gwamnatin jihar Ribas, ya tabbatar da ikon karbar harajin VAT a hannun Hukumar Tara Kudaden Shiga ta Kasa.

Ya ce hukumar tara kudaden shiga ta kasa ce ke tara harajin kafin rigimar ta taso, wanda gwamnatin jihar Ribas ta kai kara zuwa babbar kotun tarayya.

Kamfanin Dillancin Labaran ya bayar da rahoton cewa gwamnatin jihar Ribas ta bukaci Kotun Koli da ta soke hukuncin da Kotun daukaka kara ta yanke a ranar 10 ga Satumba na cewa a cigaba da zama kamar yadda ake tsakaninta da hukumar tara kudaden shiga ta kasa kan batun karbar harajin VAT.

Leave a Reply

%d bloggers like this: