Gwamnatin tarayya ta ce zata biya Naira biliyan 22 da miliyan 172 a matsayin alawus na ma’aikatan jami’o’in Najeriya

0 72

Gwamnatin tarayya ta ce zata cire tare da biyan Naira Biliyan 22 da miliyan 172 a matsayin Alawus Alawus na ma’aikatan jami’ain kasar nan a ranar 30 ga wannan watan.

Ta kara da cewa tinda dadewa a cikin kasafin kudi na 2021 aka amince domin a biyasu wadannan kudaden.

Zakalika gwamnatin ta sake tabbatar da cewa zata fara biyan kudaden farfado da jamai’oin kasar nan Naira BIliyan 30 daga nan bada dadewa.

Ministan kwadago da samar da ayyukanyi na kasa Senator Chris Ngige, ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis, a ofishinka dake babban birnin tarayya Abuja. A lokacin dayake tataunawa da kungiyyar malaman jami’oi ta kasa ASUU.

Wannan ganawarta bangarorin biyu, sunyi ne domin sake tinawa gwamnati yarjejeniyar da sukla cimma a watan Disamba na 2020, da kuma matsayyar da suka cimma a ranar 2 ga watan Agusta na 2021.

Yayin dayake tattaunawa da manema labarai bayan kammala tattaunawar ministan yace, sun cimma matsaya mai haske a taron, tare da tattaunawa akan batutuwa masu mahimmanci guda 6 a lokacin taron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: