Gwamnatin tarayya ta fara rabon kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi ga wayanda ambaliya ta shafa

0 86

Gwamnatin tarayya ta fara rabon kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a bara, a jihoshi 16 na kasarnan.

Da take magana jiya yayin rabon kayayyakin da aka gudanar a Karamar Hukumar Miga ta Jihar Jigawa, Ministar Jin Kai da Kula da Annoba, Sadiya Umar Farouk, wacce Babban Sakataren ma’aikatar, Alhaji Bashir Nura ya wakilta, ta ce tallafi zai zama taimako ne ba biyan diyya ba, ga wadanda abin ya shafa.

Ta yi bayanin cewa tasirin ambaliyar bara kan zamantakewa da tattalin arziki, ta jawo barna da haifar da asarar rayuka a garuruwa da kauyuka da ke yankunan 6 na kasarnan, gami da karin tasirin cutar corona, inda ta kara da cewa matakan dakile bazuwar cutar sun tsananta halin da ake ciki a kasarnan.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Jigawa, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Malam Umar Namadi, ya yaba da wannan kokari tare da yin alkawarin cigaba da kaddamar da irin wadannan shirye-shirye domin amfanin ‘yan jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: