Gwamnatin tarayya ta jaddada ƙudirinta na rage ayyukan da ba a kammala ba da kuma wadanda aka yi watsi da su

0 110

Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na rage ayyukan da ba a kammala ba da kuma wadanda aka yi watsi da su kafin nan da karshen wa’adin mulkin gwamnati mai ci.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana haka a sakon da ya aike da shi wurin bikin karbar aikin hanyar Shuwarin zuwa Dutse ta wuce Kwanar Huguma a jihar Kano.

Shugaban wanda ya samu wakilcin ministan albarkatun ruwa, Injiniyya Suleman Adamu ya ce gwamnati zata bayar da isassun kudade domin samar da ayyukan more rayuwa da zasu cigaba da inganta rayuwar al’umma.

Ya bukaci masu ababan hawa da su kiyaye da bin dokokin tuki domin cin moriyar ayyukan hanyar da gwamnati take samarwa.

A jawabinsa mai martaba sarkin Dutse Dr Nuhu Muhammad Sanusi ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ma’aikatar ayyuka da gidaje da ta sanya alama a shataletale guda biyu da suke bayan garin Kiyawa domin kaucewa haduran da ake samu a kan hanyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: