Gwamnatin tarayya ta kaddamar sabon wani shirin bunkasa harkokin ilimi domin tabbatar da cewa an dawo da yaran da basa zuwa makaranta cikin aji

0 65

Gwamnatin tarayya ta kaddamar sa wani shirin bunkasa harkokin ilimi domin tabbatar da cewa an dawo da yaran da basa zuwa makaranta cikin aji.

Kaddamarwar da akayi a karkashin majalisar cibiyar bincike da bunkasa ilimi, da hadin guiwar kungiyar tarayyar turai da kuma shirin kasa da kasa na Najeriya.

Da yake jawabi a wajen kaddamarwar jiya a abuja, ministan ilimi Mallam Adamu Adamu, yace shirin na a matsayin wani bangare na farfado da harkokin ilimi na gwamnati mai ci, domin samar ingantaccen ilimi ga kowane yaro dan kasa.

Ministan wanda ya samu wakilcin daraktan farfado da ilimi da ayyuka na ma’aikatar ilimi Mallam Ishaku Abdulwasiu Adamu yace, an samar da shirin ne domin rage yawan yaran da basa zuwa makaranta a kasa, musamman marasa galihu.

Yace ma’aikatar zata sanya idanu tare da bada goyon baya domin ganin shirin yayi nasara.

Daraktan yace ilimi shine ginshikin kuma ma’aunin cigaba da bunkasar kowace kasa a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: