Gwamnatin Tarayya Ta Karbi Yan Najeria 104 Da Suka Makale A N’Djemena Daga Jamhuriyar Chadi

0 70

Gwamnatin tarayya ta karbi yan Najeriya 104 da suka makale a N’Djamena daga jamhuriyar Chadi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano dake jihar Kano a ranar Talata.

Hakumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ce ta karbi wadanda aka dawo dasu tare hadin guiwa da hakumar agajin gaggawa ta jihar Kano, da hakumar lura da yan gudun hijira, da kuma kungiyoyi da ke lura da sansanoni yan gudun hijira da kungiyar Red Cross.

Kodinatan hakumar NEMA na jihar Kano Dr Nurudden Abdullahi, yace an dawo da yan hijirar karkashin kulawar hakumar lura da yan gudun hijira ta Duniya daga N’Djamena karkashin wani shirin tallafi. Kodinatan hakumar yace yan hijirar sun hada da maza 34 da mata 18 da kuma kananan yara 52.

Leave a Reply

%d bloggers like this: